Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : shugaban Rasha Valdimir Putin da kuma shugaban kasar China Xi Jinping sun tattauna a yau ta wayar tarho, dangane ad halin da ake ciki a kasar Afghanistan.
Shugabannin kasashen biyu sun nuan takaicinsu matuka dangane da irin halin da kasar Afghanistan ta shiga, tare da tattauna hanyoyin ad ya kamata su bi wajen ganin sun agaza wa kasar.
Shugaba Putin ya jaddada wajabcin yin dukkanin abin da ya kamata domin ganin cewa kasar Afghanistan ba ta rushe ba, tare da taimakawa wajen ganin an hada kan al’ummar kasar, domin su hadu su gina kasarsu.
Shi a nasa bangaren shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana takaicinsa kan abin da ya kira manyan matsalolin da kasar Amurka ta haddasa a kasar Afghanistan, da kuam jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin hali tsawon shekaru 20.
Shugaban na China ya bayyana aniyar kasarsa na bayar ad dukkanin gudunmawa wajen agazawa kasar ta Afghanistan a dukkanin bangarori.
Sannan kuma ya dora alhakin abin da ya faru baki daya a kan kasar Amurka da kuam kasashen turai, wadanda suka mamaye kasar tsawon shekaru ba tare da sun iya tsinana musu komai ba.
342/